Lyrics

Sadiq Saleh's Production Ke nake jira Ke nake jira Ke nake jira Wai yaushe za'ayi mana aure? Kai nake jira Kai nake jira Kai nake jira In ka so sai ayi mana aure So yayi mini, kin ja mini sai na fadi Ga fah baituka zanyi miki adon kidi Ba ruwan ido, kece wacce kyawun hadi Kwan a tashi zamu hade indai mukayi aure Soyayyah ka bani na baka Burina shine nayi zama gidan ka Rayuwa ce dani za'ayi wa barka Nawa burin shine wai yaushe zamuyi aure? Aure, wai yaushe ne? Rayuwa ta kasance sabon gini Ni dake na amince, kinyi mini Koda yaushe in nazo gake nayi tuni Kiyi ta farin ciki burina ya cimmini Nawa, nawa ne, toh wai yaushe ne? Ke nake jira gidan ku in tura da komai Aure Aure Ina farin ciki ka yaba ado na So nake in kira ka mai gida na Ban baki ciki in kana kusa na Lokaci yana zuwa a sanya rana Nayi mafarki, ka zama sarki Kai ka mallake zuciya ka zam mini komai Toh wai yaushe ne? Kai nake jira Duk na damu ne Nima na kagara Zamu rayu da soyayyah ba takura Kamar hanta-jini muke a so mun shahara Bana jin kira, koko ayi dara Ko a yau a daura auren mu da kai an gama komai
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out