Lyrics

Shimfidar fuska ta wuce ta taburma Talafa mini kar so yasani jarkoma Akanki zan jure gwagwarmayar fagen fama Idan kina so nah bani babu yin rama Idan zaki kije dani Idan nai fushi ki rarashe ni Silar so na shiga baban karni Idan gani gaki sai inji ina farin ciki yamai sabuwar amarya Duk wayyon dila a daji so ya tafi dashi nayo sabuwar hikaya So na seta hankali da nutsuwa ace idan ka zarce ama amarya Nai dacen masoyiya, tana sani dariya akanta na tausa murya Mai kunya akwai ladab da biyaya Sam bata biye kawayen hanya Uwa gun rago ake wa jaje uwar gwani ko sai a dinga mata sam barka Mace mai jure akwai da babu itace ake wa take da farin cikin gida ko buka Masoyiya tana da kyau kuma bata ji da kai hakan ne yasa ake mini barka Duk wahala ta faskare, ko sananin dakon rake idan nai na bata, bata raina Santa yana cikin jinina Burina dare da rana In ganki a cikin gidana, kin zama mallaki na haka zai faranta raina Nayi na'am da hankalinki da nutsuwarki nazarinki sune a gudirina Ki sa ranki naki ne, ni bazana bar ki ba, har abadan kina gida na Zana tarerayeki so sai ni zan kula dake fiye da yadda zan ma kaina Ke kika zama hantsakina Mai girman daraja a gu na Asusun da nai yi don ke nai yi ungo ajiye min so ne a ciki da kauna Yarda ce tasa ba baki ajiya ta rayuwata nasanki da amana Idan har ina dake bani babu zulumi hakan na saka a raina Wanda ya samu kullawa a so kamar yadda kika min to so yayi masa rana Ga sako gurin masoya Karda mu maida so kiyaya Wanda ya soka sai ka so shi san gaske babu wasa a cikinsa yan uwana Karda ka maida so makamin cutar da wanda ya soka hakan zai zama barna In aka furta so gareka sai kai na'am a zuciya kar ka zagi kauna Akwai wasu yan adam sun sa a ransu babu san gaskiya babu mai amana Muyai nazari sanan mu auna Karda mukai masoyi raina Muyai so don rikon amana Masoyi yana da rana Masoyi yana da rana Masoyi yana da rana Masoyi yana da rana
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out