Lyrics

Da soyayya Da soyayya na fito nima Ayyah, ayyah Da soyayyar ki nake kwana nake tashi Ki sani a ran ki hakan kimin biyan bashi Da soyayyar ka nake kwana nake tashi Ka sani a ran ka hakan kiyi min biyan bashi Ni na saba da furta miki soyayya, ya Da kin duba a fuska da labarin zuciya, ya Bazan so ba in kika kini zansha wuya, ya Da kin furta in naji za nayo hadda Ki tunkaro cikin taro a bubbuda Da sun gan ki yanmata sai suyo guda yiriri-yiriri Da wasa ne ko gaske kalamun ka, ka Idan haka ne nayo nasara kumin barka, ka Na yarda da soyayyar ka gare ni ba shakka, ka Zan aure ka Na zam taka A dakin ka in narka ma miyar kuka Abincin ka zana kula wa dangi kar na ciko gishiri Da soyayyar ki nake kwana nake tashi Ki sani a ran ki hakan kimin biyan bashi Da soyayyar ka nake kwana nake tashi Ka sani a ran ka hakan kiyi min biyan bashi Ke nayi wa tanadi na Zaman cikin gida na Mai kwantar da hankali na Kece rabin jiki na Mu taru mu raya sunnah Tasa annabi na Zo jinin jikina Muradin raina Dace da juna Nace wa yan'uwa na Na kasa boye son ki cikin raina sai da dai ya fito sarari Kalaman ka suke sani farin ciki na jiyo dadi Rawa nayi na juya murna take sani nake kaudi Yabon ka idan akayi a gabana sai in bada kudi Soyayya ta karya da gaskiya da gani nata babu hadi Taba ka idan anyi sai nayo raddi Ganin ka cikin murna shike sani nima inji nayi fari Da soyayyar ki nake kwana nake tashi Ki sani a ran ki hakan kimin biyan bashi Da soyayyar ka nake kwana nake tashi Ka sani a ran ka hakan kiyi min biyan bashi
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out