Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Garzali Miko
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Garzali Miko
Songwriter
Lyrics
Ni kishinki nakeyi
Kishinka nakeyi
Karka kasheni
(Sadiq Saleh's production)
Ni kishinki nake karki gujemun
Kaunarki tanaso zata kasheni
Ni kishinka nake karka gujemun
Kaunarka tanaso zata kasheni
Ni kishinki nake karki gujemun
Kaunarki tanaso zata kasheni
Kaunarki tanaso zata kasheni ki tinani
Kina da tausayi karki bari ki tayani
Gani nan zuwa ga hannuna ka rikeni
Inka gangara wani hali zaka sakani?
Kishinki nake yardata zarce yar Fulani
Wanda ya tamini ke tilas zaiji rauni
Wanda ya tabaka
Nima zan masa rauni
Kaunarki ne nake jinta
Kamar zata kasheni
Zafi naso da kaunarka ya kaini kwance
Tinani nake kamar za'ayi mini kwace
Kullum ina maraba dakai na amince
In har kazo gida guna nayi dace
Ni nasan zuwanka guna wata darace
Rashinka gaskiya soyayyar zata kasheni
Kaunarki ta sakani inayin juwa
Nagane rashinki yana sani a damuwa
Ganinki ne yake sani cikin karsashi
Mahadin hakori ashe shine dadashi
Ni sai dake ko makiya sun fada
A rabamu dake wanan kumw babu 'da
Ko bani raye nasan tabbas zaki tinani
Hanuna yana rawa zo ka rike min
Komai ina bukatar ka aza min
Nasan babu abunda ke zaki hana min
Alkawarin da kikamin zaki cikamin
Arzikin cikin ido baya wuce ruwa
Sanadin ka yanzu sai in koma uwa
Kece uwar gida kuma kece kawa
A gabanki in kinaso sai nai rawa
Kaine kake ban nishadin rayuwa
Sai mutuwa dani dakai zata rabawa
Karka kasheni
Ni kishinki nakeyi
Kishinka nakeyi
Karka kasheni
Lyrics powered by www.musixmatch.com