Top Songs By Maryam A Sadik
Similar Songs
Credits
COMPOSITION & LYRICS
Maryam Sadiq
Songwriter
Lyrics
(Dee Nass Production)
Bana son komai
Bana son inji komai
In dai har ba sautin muryar kace ba
Kauna ne dadi ga duniya da fadi
Ba zumudi ga wanda bai iso ba
Indai kana nan farin ciki tana nan
Zuciya baka sata a damuwa ba
Baka sata damuwa ba
Na samu wanda rai na bai kushe ba
Ki gudu mai sa maza su sa gudu basu tsaya ba
Duk rintsi duk wuya bazan daina ba
Na gane menene baka furta ba
Kana sona ko ba haka kake so ce ba?
Soyayyar gaskiya bata buya dan baba
Dani da kai ba zamu ware ba
Damu da su ba zamu shirya ba
Mai so na bai kamata ya ki ka ba
Mai son ka bai kamata ya ki ni na
Dani da kai ba zamu ware ba
Damu da su ba zamu shirya ba
Mai so na bai kamata ya ki ka ba
Mai son ka bai kamata ya ki ni na
Gari ko yayi duhu ai za yayi haske
Bari ni dai naki ji, in naji da sake
Mai jinya burin sa ko yaushe ya warke
Banji an warke ba wanda ya sha dan marke
Taso ka wuce gaba bayan ka na take
Ba wanda ya kai ka in tafiya ce falke
Ina jin dadi in na gano ka a keke
Na tabbata baka so in koke
Daga nace "Wash"
Sai kace "Menene?"
Daga nace "Wai"
Sai kace "Waye ne?"
Wani irin so kake min ban taba gani ba
Wani irin so kake min ban taba zata ba
La-la-la-la ni ban taba gani
Haaa-ah ban taba zata ba a kaina
Wani irin so kake min ban taba gani ba
Wani irin so kake min ban taba zata ba
Wani irin so kake min ban taba gani ba
Wani irin so kake min ban taba zata ba
Ban taba gani ba
Ban taba zata ba
Ban taba gani ba
Ban taba zata ba
(Dee Nass mix)
Lyrics powered by www.musixmatch.com