Lyrics

Gani da dan salona, zanyi wa masoyiya Wacce na zaba ta kore min duka damuwa ta Gani da dan salona, zanyi wa masoyi na Wanda na zaba ya kore min duka damuwa ta Kyan tafiya a dawo, yau gani na dawo gun ki ki tarbe ni A kan ki nake ta kai kawo, a silar hakan ne yan8mata sun ka zage ni A da can ban iya so ba, yanzu gashi na koya domin in faranta miki taho ki dube ni Kowa na da rana, wanda ya soka ka so shi hakane tunani na Ko an bakanta mini, na tuna da kai nawa sai naji sanyi cikin rai na Gani da ado na bullo, don kai na cillo karda ku ja da ikon Allah shi ya hada mu Ni ban neman suna Na tsaya matsayi na Haka Allah yaso gani na Tare dake watarana Zamu je aljannah Haka shine fata na Allah kaji tausayin mu Ka rufa sirrin mu Kar makiya su dame mu Su hana ki rabe ni Ko an saba sai an jure, haka soyayyah take mun ji Ko an daure sai an jure, haka tarayya take mun ji Kai na saka a zuci ka tare, nayi murna za muyi aure Nayi sa'ar zabe zan more, can a gidan aure Babu fada ga dan koyo, in har yana koyo Girma zai taba malam har wataran ya samo Gani da dan salona, zanyi wa masoyiya Wacce na zaba ta kore min duka damuwa ta Gani da dan salona, zanyi wa masoyi na Wanda na zaba ya kore min duka damuwa ta
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out