Lyrics

Adon tafiya aka yi wa take waiwaiye Fagen soyayya na samo mai tarbiyya Adon tafiya aka yi wa take waiwaiye Fagen soyayya na samo mai tarbiyya Ehh waiwaye Tun ran da nafara ganin ki yanmata kika sacen zuciya Babu zato naji nayi nitso a cikin so nayi ambaliya Yanzu nasan na dace tunda na samo yar islamiyya Koda a kasar India ne, ni dake zanyo fariya Waiwaye Wa kai kadai naka yiwa take A rabani da kai wallahi da sake Na shirya jeka ka dauko keke Tuka mu muje duk inda kake so zan dale carrier Albishirin ki kice mini goro fari kisha labari Daren jiya nayi mafarki auren mu dake anyo dauri A zama na dake ba sa'insa har mun haifo jariri Na aje kudi tari-tari har muka je Saudia Adon tafiya aka yi wa take waiwaiye Fagen soyayya na samo mai tarbiyya Yes sir, dole na sara ma don ka zama gwarzon shekara Ka fita zakka don baka da halin yan yaudara Kai ke sawa raina yayi sanyi tamkar kankara Rayuwa in ba kai kamar gaya ne ba miya Domin murna ne haka kinga rawa ta A gare ki na zo alkhairi ne manufa ta Bawai aka ce alkhairi yafi mugunta Kowa da wanda yake so nima ga tawa gangariya Tun daga Laraba ake gane kyawun Juma'a Anyo shidar ka da kyawun hali gun jama'a Zan dauke ka in kaika gidan mu kar kace mini a'ah Kace masu aure na zakayi in sun bijiro ma tambaya Waiwaye Adon tafiya aka yi wa take waiwaiye Fagen soyayya na samo mai tarbiyya Adon tafiya aka yi wa take waiwaiye Fagen soyayya na samo mai tarbiyya
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out