Lyrics

Bude kunni ki saurara Komai ya same ni silar ki ne Naga kin dauki so wasa Kamar baki gane masoyin ki ne Zuciyata tana bugu Menene dalili na kaunar ki ne? Nasan kina sane Kina ganin yanda so ya maida ni Meke damun ki ne? Kin kasa gane a son ki babu ya ni Ammah zabin ki ne Ki so ni koko ki yada ni Duk da nasan akwai wuya in bar son ki ammah zan jaraba Zana rintse idaniya, in kauda kai kamar ma ban gan ki ba Zana jure hayaniya, bar saka zancen ki sahiba Da zaki dandana, abinda naka ji Da ba zaki barni ba, zaki tausaya mini Da zani bayyana, yanda zuci ke tsuma Nasan zaki taimaka, koda kadan ki sam mini Makaho ne ni, so ya rufe idanu na Dan Adam ne ni, akwai zuciya a kirji na Neman tabuwa nake Bani gane mai nake Sai sumbatu nake Oho, da wa nake? Al'ajab na son ki ne Dubi shan wuya nake Fita duhu shigo haske Bani hannun ki in damke Bini in kai ki shinge na Ba don hali ba don Allah zanyi ma maraba Ba don kudi ba koko domin wata daukaka ba Ba don kana dashi ba Ba don kuma ka rasa ba So domin don Allah nima Ba wai na yaudara ba Nima ka so ni ba don wani dalili ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out