Lyrics

Ina ji dake nidai masoyiya Ni din naki ne a fili har a zuciya Ina ji da kai nima masoyi na Ni din taka ce a fili har da zuciya Daga kallon farko, kika sacen zuciya Kyakkyawa kin kai mai kyawun idaniya Zuciya ta kin kama, kinji gimbiya Duk na rasa natsuwa da ganin ki zinariya Ai zan iya shafe awanni Koko tsawon makonnai Bazan gaji ba wajen kallon kyakkyawar fuskar ki Komai na yo silar so ni ban fadi ba Zana baka kulawa kar kayi fargaba Kuma ka zamto mahadi na jini Ban iya rayuwa bakai A zuciya tuntuni kayi gini Bamai iya shiga sai kai Kaine dai duk tsanani Har dangi nawa sun shaida Cikin barci na da zahiri, sunan ka nake ta furtawa Kece farko na, alaman furtawa Son ki na a raina, har abada bai gogewa Kulawa da so, ke dai ce za nayi nunawa Tunda kinka aminta dani ban bari kiyi kukawa Tabbas ni mai son ki ne, ko'a ina zan bayyana Kyawun yaba kyauta tukwici karbi zuciya Ni zana bika duk inda zaka kaini na shirya Komai zaku ce akan shi naji bani nuna alkunya Kawaye na ku min murna Na samo mijin aure Gidan sa kadai nake fata Dangi zaku min jere Ka zama uba ga 'ya'ya na Komai za zanyi muyi tare Kace min sweety na Niko in ce, "Maka baby na"
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out