Lyrics

(Kida) M. Shareefi (Kasheepun kida) Mai farin jini Yanmata ki nai mini kwarjini Kin shiga zuciyata Kin shiga rayuwata Kin zama damuwata Kece babbar kawata Dukkanin dare hakika yana da safiya Dukkan rayuwa akwai karshen ta a duniya Masoyi baya amsa suna in baida masoyiya Ni dai kun ga tawa Ta zarce ta kowa Ita ce mai ban kullawa Halinta abin yabawa Ta sani in mace komai, in raina yayi daci In jiki na yayi zafi, ta sanya min mafici Babu ya ke Banda ya ke Banda kamar ki duniya Hannu rike Dani dake A sannu mu zaga nahiya Zan hau duste da tsaunuka, don soyayyar ki yar'uwa Zan shiga kogi da rafuka, in haye kowani irin ruwa Kamar da wasa mun dauko Sannu a sannu munyi karko A yanzu na wuce bako Nine karshe, nine farko Fadi ku kara Wata da zahra Allah ya tsara (Allah ya tsara) Babu dabara (babu dabara) Nine mai kare duka A gare ki in share kuka Damina, rani, da kaka Wahalar ciki zana dauka a kan ki Kyawun ki yakai kyawu, a kalle ki dole a kara Dake idan naje yawo, samari su gan mu sun sara Don Allah taho ki taho da wuri Yanmata su tashi su baki guri Kwalliyar kice mai haske gari Bani gane kowa in kina guri Assalam-salam salama Nazo kiban ruwan zuma Cikin kauna na tsunduma Nayi wanka a korama Ba sauran cututtukan so Tunda kin fada ni kike so Ki wanke magauta da soso Munkai karshe a lamarin so Dani dake Mun tsallake An bani ke Aure dake Lalala la-la-la Oh-oh-oh oh A-ah, a-ah-ah (Okay, beat Amjad Record) Mai farin jini
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out