Lyrics

Zuciyata kin wanke 'yata ba tunani nake ba Yaki taho 'yar mama Taho 'yar mama Banda kamarki ko cikin 'ya 'yana mama Nai godiya ga Allah da yaban mai suna mama Domin itace mai 'dauke kewa in na tuno mama Taho taho 'yar mama waya taba mani ke Daina kuka share Karki manta hanta da jini basu rabewa Duhun dake cikin ido kece ke gogewa Kullun dana kalleki ina 'kara godewa Taho 'yar gidan baba Daina fushi taso, share share Burina shine tareda 'yarki na inganta Ba irinki gareni 'yata mai suffa ta Ako ina nake sai dake babbar 'yata auta Nasan kina san babanki Me zai hana mu zamo tare, tare tare Zan maki kyauta kala uku dan birgewa Ciki ki zabi abinda kikeso na morewa Amman sai kin mani al-'kawarin baki rainawa 'Dan yi dariya mana in gani nasan kin hucewa Farincikin ki shine nawa
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out