Lyrics

Majnoon a so na zamo mai hauka In warke sai an bani ke muyi aure Majnoon a so na zamo mai hauka In warke sai an bani kai muyi aure Soyayya ta kawo ni nazo Kulawar ki zan nuna kwazo A sona ki kira ni gwarzo Zan karba in kin bani kanzo Sarautar ki ce tayi tozo Ki mulke ni ban raina ki ba yarinya Mukami ka ban yayi girma In karbe shi sai nayi fama In zauna a gun ka ya dama Kazam shugaba sai na bi ma Ka sha zuma ka dan bani nima Mu kore kiyayya mu dauro soyayya Zuciyata chan ciki ke nayo sakawa Babu rana ba watan da za kiyi fitowa Tambura na kece kadai nake bugawa Kiyi ta murna zan so hakan dadin dadawa Ba abinda zan miki rowa Ko nine da kaina ki dauka yarinya Majnoon a so na zamo mai hauka In warke sai an bani kai muyi aure Majnoon a so na zamo mai hauka In warke sai an bani ke muyi aure Komai nawa ai naka ne Ko ban fadi ba kana sane A idanu na da hoton ka ne Ko na mutu ni da kai za'a binne A cikin jini-zuciya ta ne Babu mai tsaida mu cikin tarayya Ban fidda rabo wataran kin zam mini amarya Inda akwai rai da rabo kar kayi baya-baya Ga madara bani zuma zo muyi musaya Abinda ka so dole nayi ma shine biyayya In bake ba sai rijiya Kece zani bai wa dukan soyayya Majnoon a so na zamo mai hauka In warke sai an bani kai muyi aure
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out