Lyrics

Dan maliyo maliyo, maliyo baby tawa Gobe da labarin da zana baki na kauna Dan maliyo maliyo, maliyo baby nawa Gobe da labarin da zana baka na kauna Dan maliyo maliyo Baby nawa Kin shiga zuciyata, kin zauna can ciki Kin shiga rayuwata, kin kauda bakinciki Ke daya tilo, ke ce maisa farinciki To ce jan mutumin can Ya dauki jar sandar can Ya kori jar akuyar can Mai cin jar dawar can ta kusa da gonar jatau Sannan ki dawo in baki labarina na kauna Ka zama gwarzo a fagen soyayyata Kaine jigon rayuwata fahimta ta Sai dakai sahibina zan cimma bukata ta Maina ya kone Bada talle ba Jirkita min In ciwo kashi A hiyya! Dan maliyo! Talle liya talle liya talle liya talle liya liya liya liya liya maliyo liya Maliyo liya maliyo liya liya liya Dan maliyo maliyo, maliyo baby nawa Gobe da labarin da zana baka na kauna In har ina jin kishirwa Ke zan nufa ki debo min ruwa. In da zan kasance a cikin damuwa Kaine zaka yaye kuncina dan uwa Ayi shaburburwa Kowa ya bace Asha shi da kulki Kulkin kira Bana aro ba Ku bashi gida nai Har ya kawo fegin dan maliyo Fatana a gidan aure kai garkuwa Zan kare hakkinki karki damu yar uwa Natai tsarince Magarya tai min jar tsikara Yar bakin gulbi Tayi liya liya liya A yayyafa mata ruwa Ka dauko naka Ka tura daka Ka dauko dan wani kaita damfara sabara ah Maliyo! Dan maliyo maliyo maliyo baby nawa Gobe da labarin da zana baka na kauna Dan maliyo maliyo! Ah hairi
Writer(s): Abdallah Muhammad Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out