Lyrics

Wa zaya raba ni da masoyi in ba mutuwa ba? Ba zan iya misalta maka kaunar ka a rai ba Da kadan da kadan yake shiga ya zama babba Cikin kowacce rana Yana tsaga jiki na Yana kara shiga na Dama muyi aure da kai yau hubbi na Dake nayi sabo a so bazan iya canji ba Nayi miki alkawari bazan ci amana ba Kudurin auren kine a rai na yar baba Da rai na da jiki na Nake miki soyayya Ba watta diya da zana so in ba ke ba Mafarkina yaushe ne zai zamto gaske? Cikar burina kai ne ba sake Da kwalla kira na zana zo nan take Komai ka bida guna zaka samu ango na Ni a kaunar ki nayi nisa Sai dake zani numfasa Ko muna nesa munfi kusa A son ki ba za'a fini ba nima Kina nan a jiki na Dare koko da rana Yau za muyi aure dake hubbi na Soyayya ba shakka itace gamon jini Ranar dana fara ganin ka ka mini kwarjini Nayi miki sallama kin tsorata ma da gani Amsa maka nayi don in kauce wa hawan jini Anyi miki kunshi mai burge duk wanda ya gani Da anyi batu na lalle nakin nakan gani A gare ka da tsafta har yau kamshin nakan tuno Muryan ka a gare ni ta zarce zuma a dandano
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out