Similar Songs
Lyrics
So na ne fah
On the beat
Ni kece cikon mafarki
Zan bude sirrika
Kauna ce ta samu gurin a cikin ruhi ta habbaka
Burina na, na zama rumfa rana in tare maka
Komai in kana bukata guna zana yi maka
In dai har kanki ne bana tamkar war wara
Kyale duk wa'inda ke cewa zanyi maki yaudara
Ni kai ne cikon mafarki na dauri dammara
Soyayya ta gaskiya ce zamuyi ba jiran-jira
Inda abun da zan sadaukar kan so ke zana ba
In bake ba zuciya ta zatayo maraba
Yau ka tabbatar da lallai nice ba wadansu ba
Soyayya ruwan zuma bude bakin ka in zuba
Kin gama komai soyayyar a gaskiya kinyi min
Masu bida ta munyi ja in ja suka ce sun bar min
Gobe da nisa shakar iskan madara sai rani
Mai mana kuri mun san kauyen kuma mun san birni
Duba madubi kyawun ki yana dada janyo kallo
Kar kaji komai duk inda bayana sai na bulo
Masu kwallailai sun rodaka sun rasa harshen gwalo
Kowa ya taba min kai zan haka sai na cillo
Zan maki wargi mai so ya zama gwanin rarrashi
Ka iya wanka in ka motsa haka sai dai kamshi
Daina yabo na kar murna ta hana nai numfashi
Alkawari nayi nidai ban maka abun ban haushi
San ki da dadi
Ai ka zama sha daka turmin danya
Mai mana kaudi
Ai baya gaya mana girman kwanya
Kar kiji komai nisan jifa kasa sai ta dawo
Muyi hadaka in ka kawo haka sai na kawo
Jeki ki dawo
Bani sirrin ciki sai dai hanji
Barsu da bawo
In ka motsa a jiki sai naji
Share batun duk wani mai son ya mai na yankan baya
Naga kalaman soyayyar gaske ta fara bullo
Wanda ya kushe man ke sai munyi zare ban kwarya
Kar kaji komai duk wanda yake kwado ya san gaya
Mix kobincus
Ni dake zanyi soyayya
A rayuwata
Me zai sanya in bar ki? Masoyiyata
Kai daya ne kake mulkin zuciyata
Kake maganin dukkan damuwata
Kin zamto cikon buri, sahiba ta
Gidan duniya kece samuwa ta
Miye zaya dame ni? Kana kusa na
Idan ba ka na rantse sai makabarta
Lyrics powered by www.musixmatch.com