Lyrics

Ba za na barki ba Kaunarki na jikina Komai wuya da rintsi kina cikin zuciyata ya Aisha Kauna da so nake wanda ba iyaka da adadi Komai ya faru kece Toh kar ni barki domin rashinki zai sa na sha wuya Aisha In kyau ake bida Kyawun hali kama Bance da yar da zatai yake ba Komai cikar diya Wuri na zagaya Arewa na bincika Gabas da yamma na rasa wadda zatai ya Aisha Da zaki so ni da na warke Idan da danuwa kin wanke Farinciki nake in naji sunanki Aisha Mai so yake bida Kulawa da lokaci Kowa ya samu wanda ya bashi baza ya barshi ba Kauna ruwan jiki So garkuwar jiki In dai da so hakika Aisha ba zan gujeki ba In ganni ni da kezan zana garkuwa Na yarda rayuwata ta zama fansa ga Aisha Banga wani tasiri ba Na murmushi idan har baki Kamar ace duhu ba haske haka zan zama in babu ke muradin raina Idan so ya zama cuta Hakuri zai yi maganinsa Wannan batun ban aminta ba Maganin sonki Aisha Shine abani ke In aka bani ke toh zuciya zata wartsake Ke bara ma na fayyace In baki so ni ba In bani ke ba ki tabbata zani haukace Rintsi bakar wuya bazas sa in guje ki ba Banga wani tasiri ba Na murmushi idan har gaki Kamar ace duhu ba haske haka zan zama in babu ke muradin raina Idan so ya zama cuta Hakuri zai yi maganinsa Wannan batun ban aminta ba
Writer(s): Tasiu Abdullahi Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out