Similar Songs
Credits
COMPOSITION & LYRICS
Ahmad Idris Abdulkarim
Songwriter
Lyrics
(Mai atamfa on the beat)
Ke ake rika a dace
Wanda bai dake ya kauce
Ahmad da Nura mun ce
Ke icen madaciya ce
Gaskiya icen madaciya
Kowa ya rike ki baya shan wuya
Zurfi gare ki kin fi rijiya
Kuma haka basa kure ki ba
Kece cikar kowanne harafi
A kan ki ba'a duba harafi
Allah yasa na samu zarafi
Bazan rikon abinda ba ki ba
Naji dake ake ta tutiya
Ke daya ce koda da kishiya
Ayi fushi ko ayi dariya
Sunan ki daya baza ya canzu ba
Mai yin ki bashi yin tararradi
Da nayi bincike a Adabi
Ko masu rawuna da kallabi
Basu isa su kar dashen ki ba
Da kwarjini kike tagomashi
Kowa ya so ki baki yada shi
Cikin jini zuwa jikin kashi
Duk wanda ya musa ya jaraba
Rikon ki bayi jan fitar rabo
Sai dai ki ja a samu shan yabo
Mai rarrafe ki sa shi yayi dabo
Ki kanyi tallafin marar uba
Mu'amala na kanyi in dake
Sannan a zuciya na tsarkake
Sharri yana zuwa na tsallake
Ina dake ba zana fadi ba
Ni guzurin ki nayi tanadi
In na rasa ki banda madadi
Nayi rashin da bayi da adadi
Ido ba zaya tsallake ki ba
Abinda ya sani nazari
Na yunkuro na doki tambari
Na gaskiya ko za'a san mari
Ba zaya sa na furta gaibu ba
Gaskiya (icen madaciya)
Gaskiya (icen madaciya)
Gaskiya (icen madaciya)
Ka fada in fada in fada (icen madaciya)
Ka fada in fada in fada (icen madaciya)
Ka fada in fada in fada (icen madaciya)
(Mix golden ghost)
Lyrics powered by www.musixmatch.com