Lyrics

Wakar Dan Adala Musa Jidda Ba fada da malam ba daren Ba kara ma rago ba kahon Ya bi da allo yayi rubutu ya rike charbi Gun likimo shi ya bi daren duhu ya ga takaddu Dan Adala Mubi, Musa Jidda Ya ga kudade ya ga sarautu ya iya kyauta baba Kai kun ga makafi sun nufi rafi kun ki tare su Kunga toh kar a kuma Ba fada da malam ba daren Na ja kunnen ku Ba kara ma rago ba kahon Ina yake? Ya bi da allo yayi rubutu ya rike charbi Gun likimo shi ya bi daren duhu ya ga takaddu Dan Adala Mubi, Musa Jidda Ya ga kudade ya ga sarautu ya iya kyauta baba Sun bi ta jakara za su wuce kara Sai da nace su biyo ya raka su Tunda ya ankara sai su ka shekara Sun rasa mi ya tsayar da shirin su Ya saki bako yai tafiya tara Dan da shiri yazo na taba shi Dan da ya razana sai yayi mil tara Sai da ya che jama'a su tare shi Ran da ya hasala ne suka daddara Sun tafiyarsa kamar ya ranta Sun saki shirme ya saki ilimi, dadin kida Ba fada da malam ba daren Na ja kunnen ku Ba kara ma rago ba kahon Ina yake? Ya bi da allo yayi rubutu ya rike charbi Gun likimo shi ya bi daren duhu ya ga takaddu Dan Adala Mubi, Musa Jidda Ya ga kudade ya ga sarautu ya iya kyauta baba Musa Jidda mai kudi dama da hauni Kowas shigo tabbata ya gama kuri Ubansu Naziru mai nasibin buga kudi Muje dan Bello Dan Adalan Mubi jirgi Jirgin yaki sannu jirgin saka jirgi Kai ka ga tasu baba su, sun gaza komai Ba fada da malam ba daren Ba kara ma rago ba kahon Ya bi da allo yayi rubutu ya rike charbi Gun likimo shi ya bi daren duhu ya ga takaddu Dan Adala Mubi, Musa Jidda Ya ga kudade ya ga sarautu ya iya kyauta baba Allah kare malam babba Allah kare malam babba Allah kare malam babba Allah kare malam babba Dan Adala Mubi Musa Jidda Allah kare malam babba Allah kare malam babba Dan Adala Mubi Musa Jidda Allah kare malam babba Uhmm, shagundum babban limamin mu Tafiya dai ba adin ilimin mu Daddyn mu Dan Adala Mubin mu, Musa Jidda Shagundum babban limamin mu Tafiya dai ba adin ilimin mu Daddyn mu Dan Adala Mubin mu, Musa Jidda Mutane, baba na malam ne Mutane, baba na hakimi Mutane, baban mu mai Naira ne Tafiya dai babban limamin mu Musa Jidda Shagundum babban limamin mu Tafiya dai ba adin ilimin mu Daddyn mu Dan Adala Mubin Mu, Musa Jidda Ku tina dai zamani Allah ne Jama'a dai sirrin Allah ne Ku tina dai mai ilimi malam ne Addu'a dai malam sirrin na Musa Jidda Shagundum babban limamin mu Tafiya dai ba adin ilimin mu Daddyn mu Dan Adala Mubin mu, Musa Jidda Salamualaikum jama'a ta ya aka kwana? Ya aka dau kai? Ya aka sau kai? Ya su Buhari? Ya su Buhari? Yanzu garin duk ya hada rai kai yayi da suki Allahu ya kawo, waka muka zo wakar Musan mu dasauki Musan mu uban Zunnurainin dada karfi Ta kanyi salam kuga kaka mai dada kwari Haka naga maza sun sunkuya kai daga fili Mai san Addu'a ya taho malam zai zauna Addu'ar Malam tamkar yankan rai da kunji Haka zashi fada haka Allah zai mana nan ma Ya sha ya kiramu ya che sai kaga ta zaka yanda ya che Ku tambayi manyan kasar mu nache Malam Musa in ku che Jidda ta nan zancen ya wuce Sai kuji ya su zako suce Allah in yai maka baiwa zata fito fili Kura za ta kama kura A kaura zaya soma sara Musa Dan Adala, Musa Jidda babana ya daran ma tsara dukka Ga kura zata kama kura Ga kaura zaya so ma sara Musa Jidda, Dan Adali Mubi Alhajin Allah kai girma ya daran ma girma malam Dawisun zashi motsa che ma sarakan garinmu Ga gamjin zashi tashi duk sara sai a bar shi Limammin nan mai aminchi, shi ya fito bada yanchi Ba ban aka bar da babu Allah dai ya bawa Musa Ya'ya sai ya bawa kowa Ciwo yai ya bar ma Musa Ya ma aurenka Ka haiho danka Ya sanya duk ana san Musa Tashi dai zaki Shi ya biyo aiki Ya nema masu takin Ya noma kuma ya basu Musa Sa'a dai malam kaga jinin malam malamun malam Malam namu malam Musa Allah dai ya biya mu Allah dai ya biya mu Mu dai Allah dai ya biya mu Allah dai ya biya mu Da yasa munka samu musa Musa yazama uban mu, yazama kakan diyyan mu Allah dai ya karai Musa Mai zagi daina zagi, zagi daina zagi Mai duka daina duka, zagi daina zagi Idan munyi zancen uban mu sai kaga anzo gaban mu ance an yabama ma Musa Da azumin ana ta koka yunwar da tazo da chanji Shi sai ya raba ya ba wa kowa Abunchin in ya baka sai shekara ta zago kana ta chi da karko ka dafa kuma ka bawa kowa Fari dan Dan Adala Tafidan Dan Adala Zuma zakin ki bashi cuta Da ka ji kiran tafidda Magana che ta chi da bayi Tafidan Dan Adala Musa Da Sallah sai ya bada shanu Muma sai ya bamu munka dafa mu da baba harda makwabta sun samu, ladan Allah ya bawa Musa Munga maji dadi da shi da chiroma da wakili chan fadar Musa Yaya kwanan kilishi da shi da barade da garkuwan fadar Musa Mun gano jakada da jagaba ga chokali da dan chiye na Musa Ina gayya ta Dan Adala sarki ne yazo A che ma uwar fada Mai waka yazo Allah dai ya ja da kwana Musa Kakan Musa barsu su kara shirin basu zo ba Barsu da kansu ashe ilimin Allah ba nan ba Toh koh gaban wakar ka da mun fara tai karko, (In sha Allahu) Jama'a dai ka biya su Hakimin mu, mu ya biya mu Ai kowa ya biya shi Musa kayin mota Ya bada gidan kwanchi Ya kara maka mota Ya mota kan mota Mai gonar mota Allah dai ya kara kauna Musa, (Amin) Daula dai Dan Adala Daular ka ta kara daula Ka girma ka kara daula Allah dai ya kara nisan kwana Dan Adala Mubi Amin Allah ya sa mu dace
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out