Lyrics

Ai wannan kidan da dadi ba Wanda naiwa Sai Rahama Na doka tambura na ga jita Tana Kiran Rahama Kowa yazo yaji ba laifi kuna da Rahama Girma Yana da Rana lalle ranar shi kin gani Rahama Ataka a hankali ga zarewa Tana fadin Rahama Sannunki gimbiya sannun ki adala Rahama Sannunki jaruma kuma sannun ki malama Rahama Sannunki hajiya Mai Dan abin biki Rahama Mata suna fada baiwa kinfisu gimbiya Rahama Mai kyau da kwarjini ga hakuri gurin Rahama Girmanki naki ne waye yake gudun Rahama Ki kyale mahassada Kinga kinsamu daukaka Rahama Aboka da makiya wannan dai lokacinta ne Rahama Jirgi yazo gari bakomai zaiba zaya dau rahama Ga yar sarakuna rahama sannan diya ta malumma Giwa nace dake kin dara mata dubu dubu rahama Mata adon gari bawani birni da babuke rahama Tauraruwar gari haske da walkiya rahama Kwarkwasa nada haushin kifi shikwa yana ruwa rahama Boka yana da haushin malam, malam yana da alfarma Tafiyan gari da nisa wanan lallai a barwa rakomma Ke addu'a ashe tuntuni an amsa addua'r rahama To ga kiran danai shima zai amsu gunki ke rahama Sallah kina tayi ki kara da nafula rahama Sannan wajen shiga hijabun rufe jiki rahama Kowa ki gaidashi girmanki nakaine rahama Ramattu gimbiya koko muce dake rahama Aljanna nada su na amman sunanta ma gidan rahama Ramattu gimbiya koko muce dake rahama Ki taka ki rausaya kinji wannan kidankine rahama Ali jita ya gaida ke, surukin halinki ne rahama
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out