Lyrics

Amarya taso zauna a gefen ango Domin kun dace gareki ya zam jigo Ki lallaba Mukutar domin zuma tafi rago Auren soyayya da ba a yin jayayya Zainabu amarya Hamisu ne mai waka Nazo ne gareki da wata babbar saka Bude kunnen ki Amarya ga wata waka Kinyo aure ne muna ta sa albarka Dani da Mudan Auta shi ya sa nai waka Amarya yar gidan albarka Ki zauna Gudar da muke zamuyo tagwayen aure Burin mu ki zauna gidan mijin ki ki tare Zainab mama amarya kiyi ta fesa turare Mukutar chairman dake da shi a yau an daure Murna muka zo mu taya ku ranar aure Amarya koma jikin mijinki ki zauna Idan kinyi hakan soyayya ta zama kauna Ranar wanka cibi dole sai an nuna Salisu yaro nawa yai rawa dan murna Amarya Zainabu mama yau ga rana Mun shaida angon ki baya gugar zana Mukutar ango yanzu ka darama gwarro Kayi auren so a yanzu ka fasa taro Ka fi su Ghali Dorayi suna nan a sauro Muddasir Auta na san ya nan a hanya Ya kusa aure tunda shi yana soyayya Amarya ga tamburan mai waka Buri na a ce ki tashi ki taka Ango ka zo ka dan Albarka Ga abokane suna gaishe ka Isma'il Barewa ban gangar ka Mamana a yanzu zan gaishe ki Maman amarya Maman ango dole yaban ki Ranar aure Yau ne ake bikin 'ya'yan ku Soyayya sillar zama da amana Nan zani tsaya nima gida zan koma Sunana Hamisu S Yusuf ne Breaker ni din na yan Dorayi ne Sai wata rana yan uwa na barku lafiya
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out