Lyrics

Tabdi jan A Zango Tabdi jan Hmm, kwalwalniya Adamu ka zamo kwalwalniya (namiji mazan kwarai) Kwaikwaiya Zango ka zamo kwalwalniya ٱللَّٰه لآ اِلَهَ اِلّا اللّهُ مُحَمَّدٌ رَسُوُل اللّهِ Eh mai wasa da damisa gangaci yake Ku bamu guri kar ku tsai damu tsakiyar ganuwa Eh tafiyar fari ai da ta-ta-ta mun isso Da kadan-kadan Zango na karaso Tun a garin mu kowa ne ya kaso A taka rawa babu wanda ya issa ya karaso Da nazo garin Plateau nan na daso Tun a unguwa muke wasan kwaikwaiyo Ta kamfanin Sale shine fa Zango na biyu Nai yan dankali kwatance da kayo Layin zana kadan in ka waiwaiyo Kai tun daga makarantar secondary nake rawa A lokacin nasamu suna Usher Hmm, kwalwalniya Adamu ka zamo kwalwalniya (namiji mazan kwarai) Kwaikwaiya Zango ka zamo kwalwalniya Hagen dala ba shiga birni ne ba Kai da ke sauraro ka budw kunayenka Kazamo mutum kamar ni dan zango Mai masoya ai ko'ina ayo kaunarka Wahala ta duniya sai ka sha sanan Sanan dadi yazo ya tinkare ka Daga fari zaka fadawa damuwa Za kai gamo da kunci na rayuwa Inuwa zata zam kamar rana dan uwa Kullum kana cikin yunwa da kishin ruwa Ba mai baka ko kobo babu gudumawa Babu aboki bare ma budurwa Amma in ka sanya Allah a gaban ka Zaka dace ta ko'ina ayo zancen ka Hmm, kwalwalniya Adamu ka zamo kwalwalniya (namiji mazan kwarai) Kwaikwaiya Zango ka zamo kwalwalniya A da idan ina tafiya babu mai kula ni saboda babu wanda yasan ni Sam babu tsangoma, ba sharri da tone-tone Kuma babu wanda zai zage ni Waya tana hanu na tun safe babu flashing Kuma babu wanda zaya kira ni Amma yanzu na shigo sabon rayuwa Duniya ta samu sam bani da damuwa Ina hawa motata sabuwa Nai aure ga gidana ga yan uwa Yan mata da yan maza bata tururuwa Amma abin takaici yau Zango banda inci Ta ko'ina babu sukuni Hmm, kwalwalniya Adamu ka zamo kwalwalniya (namiji mazan kwarai) Kwaikwaiya Zango ka zamo kwalwalniya A kwan a tashi dukanin yan uwa sunata korafi Zango baida zumunci Idan an kira a waya, ban daka ba, ace dani banda mutunci In an kirani aiki na nuna babu hali, ace dani banda karamci In nayo kwalliya ace nayo takama In nai mota ace na cika fankama Mahasada kullum na tsangoma Burin su dai ace nayo birgima Adamu Zango sai ace na cika rigima Komai nayo cikin wanan duniya Yarima sam bani burge ko wanene Hmm, kwalwalniya Adamu ka zamo kwalwalniya (namiji mazan kwarai) Kwaikwaiya Zango ka zamo kwalwalniya A waya akan kira ni akalla sau dari shida Kullum aradu banda sukuni Ina kida ga waka ga shirye-shirye ta ko'ina a fani-fani Ya yan uwa abokai da dukanin masoya Ina roko ku dai yafe ni Kuyi tinani kumin uzuri yan uwa Kullum cikin tinani nake mai yawa Nauyi yayai min yawwa nashiga mantuwa Ku taimaka ku fid dani a damuwa Masoya na ku dau hakuri yan uwa Nai godiya gurin mai sona uwa Komai girmar masifa masoyi bai barinka Mu so junan mu domin Allah Hmm, kwalwalniya Adamu ka zamo kwalwalniya (namiji mazan kwarai) Kwaikwaiya Zango ka zamo kwalwalniya Kowani dan adam gun Allah da jarabtarsa Amma wadansu sun dame ni Ance Zango ya cika aure yana sakin mata don kawai yana zamani Sun manta cewa mai daki shi yasan gurin dake zuba gidansa fani-fani Toh kunji daukaka kenan nahiya Jiya kai kuka a yau kuma dariya Ka shuka ba mai fadawa duniya In kai kuskure a talatta wa duniya Ba mai baka shawarar hanyar gaskiya Sai dai karya da jin dadin duniya Kowa burinsa yazo gunka yasha miya In wahala tazo ya tsare yayai buya Wasu sun take laifuka nasu a duniya Sun hango naka sun yada a duniya Toh kunji daukaka dadi daukaka da yaji Ku sanya hankali mizani Hmm, kwalwalniya Adamu ka zamo kwalwalniya (namiji mazan kwarai) Kwaikwaiya Zango ka zamo kwalwalniya ٱللَّٰه لآ اِلَهَ اِلّا اللّهُ مُحَمَّدٌ رَسُوُل اللّهِ Eh mai wasa da damisa gangaci yake Ku bamu guri kar ku tsai damu tsakiyar ganuwa
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out