Lyrics

Ban gudunki kowane yanayi kinka samu kanki a nan nanke Ban gundunka kowane yanayi in kasamu kanka a nan nake Ban gudunki kowane yanayi kinka samu kanki a duniya Ban gundunka kowane yanayi in kasamu kanka a duniya Zan kula da ke Alkawari nayi wa kaina Na aminta cewa in mutu ke kau ki zauna Zani zauna da yunwa ke kau kici zanyi murna Ko ana harbi Ko ana harbi Ko ana harbi da bindiga zan shigo in zo in ganki ke Abinda zaka chi Inyi shi babu ja na sallama Kasa ni zana yi Ko rafi kace in tsunduma Nauyi bazan ji ba Ko tsauni kace in kinkima Ana ruwan sama Ana ruwan sama Ana ruwan sama Ungo lema na aminta nikuma injike In dai akwai kula Soyayya na kara karuwa Sai anyi shakuwa ake bayyana wa juna damuwa Ra'ayi hali daya Shi ke haifar da jituwa Ina dasaki a zuciya Babu wata macen da zatazo har ta hake Sa'ar rabbi shi ke bayarwa Soyayyarmu shi yayi hadawa Hakuri ga wanda ke nemawa A sannu watarana zai samawa Addu'a Allah nake ta rokawa Aurenmu za'ai daurawa Komai nake bida Babu mai mani Rabbi kai kadai ni na rike Ban gudunki kowane yanayi kinka samu kanki a duniya Ban gudun ka kowane yanayi inka samu kanka a nan nake
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out