Lyrics

(Sultan with the beat baby) Ga sako ina fada Ku fahimta mahassada Indai lokacin kane Nasara ba zata barka ba Ga abu nan a zahiri Kuje ku fada gari-gari Jirgin Nuhu bai bari Wasu ne basu gane haka ba A gun Allah nake bida Rai na shi ya da dada Ya yarje na shimfida Haushin ku ba zaya kai ku ba Ga magana a hankali Makaranta ko a dandali Hannun mu yana da cokali Mu dangwala ko ba da son su ba Toh har yau gamu nan tafe Da ƙafafu babu rarrafe Waka zamu wallafa a ji dadi ba za'a kita ba Bauna saniyar sake Zaki na wurin rake Ya wani zai fututtuke Yayi ta fushi shi ba uban mu ba Yanmata yaya za ayi? Ko kin shaida saurayi? In da kudi yazo ayi In kuma babu ba za'a bashi ba Bature mai kamar kare Maganar zamu warware Mune ke ta jan zare Don waka ba za'a fimu ba Kura mai wayan kwadayi Ba'a son ta ko da dai Abu zancen mu ɗai da ɗai Gwarawa basu gane kanshi ba Timbele ga tunkiya Nono sai ga saniya Mai son jarumar diya Ba zai ce bai zo da ahu ba Ni nayi batu a zahiri Dan kauye da dan gari Ga sanda ta zunguri Mai yawo ba zaku gan ta ba Ni nagode wa Rabba na Yayi baiwa na adana Na guji duk abin tsana Tarihi bai zo da aibu ba Soyayya nake nufa Ciki ba a rufa-rufa Kar wani da ya zurfafa In ba'a gane asalin sa ba Magana ce da korafi Gun makiya da hadafi Sai yai ta kan su zaya fi Ba tilas sai sun biyo mu ba Hutu ba na karuwa Juya bata haihuwa Aure inda gurguwa Bai dace da a kaita nesa ba Yau mune da lokaci Mun tserewa firgici Nasarori muke ta ci Har abada ba zamu fadi ha Gun Allah muke bida Su boka suke fada Sun ce zata da dada Ni nace ba zaya kar mu ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out