Music Video

Zuciya Da Numfashi (feat. Sadi Sidi Sharifai)
Watch {trackName} music video by {artistName}

Credits

COMPOSITION & LYRICS
Maishadda Global Resources
Maishadda Global Resources
Songwriter

Lyrics

Zuciya ce da numfashi Ke amo mai zubin koke Dake tun babu komai Shine mafarin bayyyanar so Toh ashe lalai ko so Gurbi mazaunin ruhi yake kwana Hmm-mm-mm-mm Tafsilin so da zanyi Akan haduwar kaunar farar ta daya An gayyacen biki A kace nai yo waka ta soyayya Ina shirin na fara Sai ga wata yarinya zubin Allah Kirar masha Allah Har sai dana ce subhanallah Na tsarkake Allah Sai tace dani "Malam kasa min wakar izina" Sai na fara Izina ta Ke nake nuni Karka guje ni Dan zamani Mai kyan launi Zan zama tsani Samun sukuni Taho Taho Izina Nayi nuni dakai sahibi na Kai nake so a raina Ji tausai na, na, na Karkato Na mato Ceto Zakayi Wakar izina har sai da ta kare Ni da ita junan mu mun ware Nai zaton haduwar mu ta kare Toh ashe dai hakan ne mafari Kuma gashi an kusa auren ta Jini na sarauta a taken ta Wai taya za'a faro? Mai kallo mai sauraro Ku biyo ni bashi na faro Cigaban zan kwararo Zuciya ce da numfashi Ke amo mai zubin koke Shi mafari na so take Shi gamon akwai hasashe na
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out