Lyrics

Duniya Bash Neh Pha Duniya Duniya Life Hour-hour wasu plasma wasu yakubu tv Mutane daban daban Wani babu gemu babu tinbi Tsoho zai fada ma duniya a da sune sababi Halitu ma sun banbanta Gefen giwa gefen zabi Bai faru ba A ce wa kowa layi daya zai bi Indai kai kaje a jirgi wani trailer ne zai bi Wani ci da gwamnati Wani da saida kayan baby Wani ya bi hanyar office Wani hanyan gona zai bi Wani in ya ci ya koshi takan naman kaza zai bi Wani zai ci zogale wanda kudadai suke bi Wani san duniya ne ma yasa kun daina sa hijabi ne Neman kudi hadda yankan kai kun manta ma hisabi Hanyar hawaiwa na fito hanyar mutuwa ne zan bi Duniya karama che kamar ramin da tsinke zai bi Kana jira sai ka tsufa zaka ce wai Allah zan bi In ka bi baba da Mama kaine Albarka zai bi Kana kwana a katifa wani tabarma shi zai bi Kana neman na sutura wani na abinci zai bi Layin da Allah ya zana dolle shi ne bawa zai ba Kar ki hallaka ni (duniya) Kina rikita ni (duniya) Kina da dadi (duniya) Kai baki da dadi (duniya) Kar ki hallaka ni (duniya) Kina rikita ni (duniya) Kina da dadi (duniya) Kai baki da dadi (duniya) Dolle jinjiri zai tsufa zai kodai ya yamushe kaga kamar an matsa paper Ya yan samari na tsiya dan jinin su yana kumfa Minene bahaushe ya fada? Komai nissan jifa Wasu don talauci duniya suna cikin masifa Wani ba Ido ba kafa amman ka duba kai fa Wani ba hannu ba kunne bale ya tuka tifa Duniya wani na kauye inda babu wutan nepa Nazi zuma Ban dutsen maganganu in jefa Wasu sun dauki gulma a nan da chan suje su jefa Gwanda kai ka ci tuwo Wanda ya rasa fatai fa Kar ran ka ya bacci kana keke in kaga bespa Duniya ce zaka je ka sai motor kuma ka pimper kayi gida ka sa iyalin ka Ka kulle kofa wani bai da shi gidan haya a nan yake ta tsufa Kuna san labarin duniya ku ban biro da paper Wani ba gida sai karin aure da tsabar masifa Wai Sallah ana jiran mai kudi Lahira akwai fa tsakanin mu da banbanci Rediyo da woofer dan mama bakin magana Yau dolle zaku sha fama Kar ki hallaka ni (duniya) Kina rikita ni (duniya) Kina da dadi (duniya) Kai baki da dadi (duniya) Kar ki hallaka ni (duniya) Kina rikita ni (duniya) Kina da dadi Kai baki da dadi Bash Neh Gwanda kai samu haihuwa Mai zagin kashin yaro, yi tunannin Wanda bai da shi ga shekaru sun karu Yanzu kai kafara girman kai dan kazama tauraro A che dai yanzu a ko ina Kune fasa taro Ka wuce shan ruwan rijiya Sai dai ruwan faro Ka bar yan uwa da abokai A chan da durin baro Kar ka manta yan uwan ka ma Akwai ma tallan goro Dan mama ku bani lokaci Yanzu zan je in karo Kar ki hallaka ni Kina rikita ni Kina da dadi Kai baki da dadi Kar ki hallaka ni Kina rikita ni Kina da dadi Kai baki da dadi Music at 360hausa dot com dot ng
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out