Lyrics

Eh matata ce ko kwa 'ya ta? Bakon lamari a rayuwata Yazo min banyo zato ba Gani ina auren 'diyata Ah mijina ne shi ko Ubana Bakon lamari a rayuwata ta Yazo min ban tsallake ba Gani ina auren ubana Mata ko 'ya sai ku duba 'Ya dai da uba babu aure Bakon lamari inya taso A shiga hali matsananci Eh nashiga tsanani a rayuwata ta duniya inane ni zan sanya kaina Aure ne dan raya sunna da kyan niya zaya zaman baci na suna Duk mai rai bai iya haurewa 'kaddara mu dinga tunatarwa da juna Yanzu ina zanje na kwana? A ce miji nake a idanu na 'diya ta Mata ko 'ya sai ku duba 'Ya dai da uba babu aure Bakon lamari inya taso A shiga hali matsananci Eh so mai saka yayi 'dauri dabai-bayi ya kai ni ga auren ubana Babbar matsalar da nai shigewa itace harma da ciki nai jikina Dan dayake yawo jikina idan na haihu yazama 'kane kokwa 'dana Ga mutuwa dai ba a santa amma a yau ni ita kaina nakewa fata Mata ko 'ya sai ku duba 'Ya dai da uba babu aure Bakon lamari inya taso A shiga hali matsananci Innalillahi wa'inna ilaihi raji'unn Allah sarki na duba Al'amarin nan daya taso ya faru ne bada sani koda so na rai ba Amma yazo dole kuka idaniya bansan yaushe zaya kau ba So na iyaye dasu da 'ya'ya Amma a yanxu sai nafi so in bata rata Mata ko 'ya sai ku duba 'Ya dai da uba babu aure Bakon lamari inya taso A shiga hali matsananci Eh nama tsani duniya gabadai Idan da rai yazanyi da 'yan sa ido da kallo? Ga kuma cuta ta laulayi in ta tashi ko gaban jama'a zana hau kumallo Zo kuga mata kuma 'ya a gurin ubanta koda sai ai ta jefa 'kwallo Wayyo ni inta rausa kuka Ina tuna nayi asarar rayuwata Mata ko 'ya sai ku duba 'Ya dai da uba babu aure Bakon lamari inya taso A shiga hali matsananci Buri na uba inya haihu yasamu 'ya da ta tasa yayi mata aure Nima da hakan a rai na, nasamu 'ya na bata miji suyi zaman su tare Yau matsala ta shigo jikina tai tabo da ban iya gogeshi ko na sare Na riki 'ya ta zama na aure Yanxu ma idanuna na gudun su ganta Mata ko 'ya sai ku duba 'Ya dai da uba babu aure Bakon lamari inya taso A shiga hali matsananci Eh ni 'ya ce wadda aka haifa da aure amma kuma yau nai daban da saura Domin sauran suna da dama na rayuwa da zasuyi ba tsangwama harara Allah masanin zahiri na da badini komai a garan kai ka tsara Kawon 'dauki na daina fama Dan gani zaune na rasa 'yanci irin na mata Mata ko 'ya sai ku duba 'Ya dai da uba babu aure Bakon lamari inya taso A shiga hali matsananci Eh mata tace kokwa 'ya ta? Bakon lamari a rayuwata Yazo min banyo zato ba Gani ina auren 'diyata Mijina ne shi ko Ubana Bakon lamari a rayuwata ta Yazo min ban tsallake ba Gani ina auren ubana Mata ko 'ya sai ku duba 'Ya dai da uba babu aure Bakon lamari inya taso A shiga hali matsananci
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out