Top Songs By Nura M. Inuwa
Similar Songs
Credits
PERFORMING ARTISTS
Nura M. Inuwa
Performer
COMPOSITION & LYRICS
Nura M. Inuwa
Composer
RR
Songwriter
Lyrics
Kama da wane batayi wane ba
Zaman gida ki zauna
A hankali abunda duk kikeyi shi zanayi
Kama da wane batayi wane ba
Aikin da duk kasa kanka zakayi
Na tabbata bazai gagare ni ba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
Aikin ki bai wuce dora dan tsaki
Ki sarafa na dawo nazo mu ci
Cikin haka miye daya da zai wuya
Ya gagare ni nai miki tsokaci
Jollof na shinkafa ne zaiyi wuya?
Ko dambu ki kawo madambaci?
Harma daka da surfe cikin gida
Shima hakan bazai gagare ni ba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
Miye kake a office?
Da zai shige min duhu a kai na da ilimi
Sai da ku dauki paper ku cicike ku soke da bakin alkalami
Akan haka muje zan iya da kai
Na tambaya ya kan zama malami
Ni macece amman kwai kamar maza
Duk kin rufe baki na yan uba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
In kin haka ni kin hutar dani
Tafi office na zauna cikin gida
Kafin kije ki dawo na tabbata
Komai kike bidda zana har hada
Raino yana da sauki
Wajen kula ki aje yara ni zana mai gada
Tunda na kokari na da kanki ma
Zaki gane kinyo kure gaba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
Eh kuri kake ka taka a hankali
Zaifi kyau ka bar nuna takama
Ni da kai mu bar yin cece kuce
Tunda ga gwani babu gardama
Mu buga mu kara dani da kai
Munga wanda zaizo ya sallama
Ganin ido surfe bashi yin wuya
Amman raggo bazai iya yinsa ba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
Ba a gane mai sai an gwada
Karfin hali yana nan a zuciya
Zan dauki naki nima na baki nau
Domin na kalli kwalla a rijiya
Gudu ya asara ga jarumi nasan gareki ni zanyi dariya
Koda munyi baki cikin gida
Abincin su ni zana rarraba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
Ba girin-girin ba ka samar da mai
Idan nace a ce ayi magani
Kallan kitse kakewa rogo
Kasan anyi ankarewa da kai tuni
Ina tunan tun ka daga ta
Bai yunwa sai dai anyi san sane
Tunda hakan kakeso muje muyi
Akwai fari bazan hane ka ba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
Kama da wane batayi wane ba
Zaman gida ki zauna
A hankali abunda dai kikeyi shi zanayi
Kama da wane batayi wane ba
Aikin da duk kasa kanka zakayi
Na tabbata bazai gagare ni ba
Kama da wane batayi wane ba
Aikin na wane in wane zaya yi
Da wahala bazai kwaci kansa ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com