Lyrics

Kama da wane batayi wane ba Zaman gida ki zauna A hankali abunda duk kikeyi shi zanayi Kama da wane batayi wane ba Aikin da duk kasa kanka zakayi Na tabbata bazai gagare ni ba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba Aikin ki bai wuce dora dan tsaki Ki sarafa na dawo nazo mu ci Cikin haka miye daya da zai wuya Ya gagare ni nai miki tsokaci Jollof na shinkafa ne zaiyi wuya? Ko dambu ki kawo madambaci? Harma daka da surfe cikin gida Shima hakan bazai gagare ni ba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba Miye kake a office? Da zai shige min duhu a kai na da ilimi Sai da ku dauki paper ku cicike ku soke da bakin alkalami Akan haka muje zan iya da kai Na tambaya ya kan zama malami Ni macece amman kwai kamar maza Duk kin rufe baki na yan uba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba In kin haka ni kin hutar dani Tafi office na zauna cikin gida Kafin kije ki dawo na tabbata Komai kike bidda zana har hada Raino yana da sauki Wajen kula ki aje yara ni zana mai gada Tunda na kokari na da kanki ma Zaki gane kinyo kure gaba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba Eh kuri kake ka taka a hankali Zaifi kyau ka bar nuna takama Ni da kai mu bar yin cece kuce Tunda ga gwani babu gardama Mu buga mu kara dani da kai Munga wanda zaizo ya sallama Ganin ido surfe bashi yin wuya Amman raggo bazai iya yinsa ba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba Ba a gane mai sai an gwada Karfin hali yana nan a zuciya Zan dauki naki nima na baki nau Domin na kalli kwalla a rijiya Gudu ya asara ga jarumi nasan gareki ni zanyi dariya Koda munyi baki cikin gida Abincin su ni zana rarraba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba Ba girin-girin ba ka samar da mai Idan nace a ce ayi magani Kallan kitse kakewa rogo Kasan anyi ankarewa da kai tuni Ina tunan tun ka daga ta Bai yunwa sai dai anyi san sane Tunda hakan kakeso muje muyi Akwai fari bazan hane ka ba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba Kama da wane batayi wane ba Zaman gida ki zauna A hankali abunda dai kikeyi shi zanayi Kama da wane batayi wane ba Aikin da duk kasa kanka zakayi Na tabbata bazai gagare ni ba Kama da wane batayi wane ba Aikin na wane in wane zaya yi Da wahala bazai kwaci kansa ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out