Top Songs By Moussa Yaro
Credits
COMPOSITION & LYRICS
Moussa BOUBE HAROUNA
Songwriter
Lyrics
Eh boye abin cikinka to karda ka tona
Ka kuka waya kyautu damkawa amana
Wani ka bashi bai gudun aika hiyana
Kula gaban ka baya ta barka ka auna
Ance rabon maza
Baya shiga dawa
Kuma so gamon jini
Dangin shi mutuwa
Wasu sunyi sun gani
Sun nemi afuwa
Ni nau na tsansane
Zan kauda tsakuwa
Eh masu shiga shara kan hadari suke
Watakila a yarda
Shi kuma damake raina kama yake
Kaga ya rike sanda
Shi hadarin sama in kaga an fake
Da ruwan cika randa
Duk maganar baka kan adadi take
A tsakar wasu suda
A gani a baya-baya kaine daga fari
Na kasa shi ya boye mu mun wuce gori
Mai biya karya-karya baya kafa jari
Mai iya kai makwarya shike rufe sirri
Fatan arziki
Sai dan arziki
Mu mun karkare, har an sha biki
Tsarkin zuciya shine kyan jiki
Ni na bayyana an ban mallaki
Da haka duniyar take aika misali
Wani abun akanyi ko babu dalili
Wani ka kan shi bai hawa ko a sikeli
Ka iya naka bai wuyar warware kulli
Lyrics powered by www.musixmatch.com