Lyrics

AMG Boy Records So da kauna dadi, ni kece a gaba na In bada raina fansa indai so zai mini rana Gani gaki a fili, nasan kinsan uzuri na Son ki yafi mini komai na mallake ki kece ra'ayi na Bani hadaki da kowa ke kadai ce tal a gida na Zana faranta miki rai, tunda dai kika zo alhali na Bani ji bani gani kan ki ko za'a batan suna Ke nake kallo, kallo na soyayyah mai dadi (Eh mana) A sonka nayi sa'a Don nasan kana da da'a Don Allah karka barni ka so ni don gujewa sa'i Gangan jiki da ruhi, ka shiga chan ciki ka zauna Kace dani mu zaga rannan sai nayi dan kara'i Na bar ciki da yunwa, na soka ba adawa Kowa shirin shiga tsakiyar mu rannan akwai bala'i So ne cikar muradi, kasan na dade da son ka Garin ku zani koma, nidai nayi rayuwa dakai yafi min Wayyo rayuwa da soyayyah Buri ya cika, tunda na gan ki a zahiri Na koma kamar tamkar yaro jinjiri Niko idan har babu kai, kasa na zanji ina jiri Na shirya na mallaka maka komai so bai jin bari Ki damu dani zan warware in tashi sahun almajiri Naci bakar wuya, a son ki na kwana a garari Kai nafi so duka duniya zan so kayi mini uzuri Ba na biyun ka zuciyata kai tafi marari Zo kiji sirrin zuciya, sirrin zuciya Kece zahiri sannan kece badili
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out