Lyrics

Mama ayye-ayye Mama ayye-ayye Mama wayyo Mama iye Mama uhmm Mama oh-oh Mama Kin rikirkita min tunani na Kai son ki ya shiga kalbi na Mama yee, Mama yee Ya Mama hasken rai na Mama yee Mama yee Mama kifi guda a cikin rafi Mama yee, Mama yee Mama kaunar ki ta shiga ruhi na Mama ayye-ayye Mama ayye-ayye Mama wayyo Mama iye Mama uhmm Mama oh-oh Mama Kai mabiyin duka waka ta Kara sauti kan murayan ka Watarana a daki na Ina a kwance katifa na Amo nake ji na tashi Ashe kara ne na waya na Sai na firgita na tashi Na farka bacci na zauna Sai nace, "Waye wannan yake ta faman damu na?" Sai na dauka na duba ba number kuma ba suna Na canza fuska nayi tsaki na kara jawo bargo na Nan na koma na kwanta don bacci ne a idanuna Na riga na sha aiki ga gajiya gabobi na Sai na sake jin sabon kara yana ta kuskure kunne na Mama yee Mama yee Ya mama hasken rai na Mama yee Mama yee Mama kifi guda a cikin rafi Mama yee Mama yee Mama kaunar ki ta shiga ruhi na Ku tsaya kuji dan gina Shin wai wake damuna Baya ko jin tausayi na Don ya hana inyi bacci na Na duba kuma ba suna Yana shiga mini hakki na Mama yee Mama yee Sai na dau waya ta na danna Sannan na kara a kunne na ("Hello") Sallama bisa tsarina Shin wai wake damu na? Sai tace "Adam Zango Wa'alaika masoyina Abin tunanin ruhi na Ai yanzu zaka ji suna na" Sai tace "Nice mama, yanzu zaka ji sirri na" Mama yee Mama yee Ya mama hasken rai na Mama yee Mama yee Mama kifi guda a cikin rafi Mama yee Mama yee Mama kaunar ki ta shiga ruhi na Mama yee mama yee Kin rikir kita min tunani na Kai son ki ya shiga kalbi na Mama yee Mama yee Ya mama hasken rai na Mama yee Mama yee Mama kifi guda a cikin rafi Mama yee Mama yee Mama kaunar ki ta shiga ruhi na Mamaye mamaye Saboda dadin muryarta Sai na goge idanuna Nayi godiya gun Allah na Don naji ta fadi sunana Mamaye, Mamaye Sai tace "Adam Zango Nima halittar Allah ce Ba kamar ka ba mai sona" Sai nace "baiwar Allah Mai kike nema guna? Waya baki fa lamba na Kika kasa kiran rana Sai cikin dare kika damu na?" Mamaye mamaye Sai tace "Adam zango Zan bayyana maka siffa na Kar ka tsorata mai sona A hankali kaga hali na" Mama yee mama yee "Ni aljana ce ba shakka Ammah ina da tsoron Allah na" Sai na firgita dangina Na kauda wayar a kunne na Bacci na sai ya kare Sai sake-sake a ruhi na Sai nace "wayyo Allah, nayi gamo fa a harka na" Mama yee Mama yee Ya mama hasken rai na Mamaye, Mamaye Mama kifi guda a cikin rafi Mama yee Mama yee Mama kaunarki ta shiga ruhi na Mama yee mama yee Harkar mutum ya sha kaina Ga aljanu kuma na bina Na kosa gari ma ya waye Don in sanar da iyaye na Mamaye mamaye Da gari yayo haske Nayi sallar Asubahi na Al'ajabi kuji dangina Na kasa karya kumallo na Ga yunwa na damuna Na kosa inga umma na Mai share mini kuka na In fada mata sirri na Domin ta share hawaye na Mamaye mamaye Nayi wanka kuma na shirya Na dau jakar computer na Na dau mukullin mota na Sannan na kulle dakina Mama, mama (wayyo) Naje na shiga mota na Da sake-sake cikin raina Ina ta tukin mota na Na rasa me ke damuna Mama, mama (eh, wayyo) Na kunna sautin mota na Domin ya debe kewa na Sai naji ance "Zango na" cikin sifikun mota na Mama, Mama Nai maza na taba burkina Jin muryar a kunne na Sai tace "Ni ce Mama Karda ka tsorata mai sona" Mamaye, Mamaye Tace "Albishirin ka fa Zango na Na zarce kowa son ka Da tausayin ka a ruhina" Saita bayyan siffar ta Gata zaune a gefe na Uhmm wayyo kaina Kyakkyawa kuji dangina Ina ma ku gane kwatance na Naso na bayyana kyawunta Ammah ya zarce tunani na Mamaye mamaye (wayyo!) Sai tace "Kaji Zango na Kar kayi mamaki na Ni yar Sarkin Aljan Baba na kuma na sona Ni da kai Adam zango Muna nan tare cikin kauna Zana barka fa zan koma Ba zaka sake gani na ba Sai dai ka dinga tunanina" Mamaye mamaye Sai ta bace daga fuska na Ina nan zaune a mota na Ammah kaunar ta ya shiga ruhi na Mamaye, Mamaye Wayyo Allah aljana yau tashiga ruhi na Mamaye mamaye Kin rikir kita min tunani na Kai son ki ya shiga kalbi na Mama yee, Mama yee Ya mama hasken rai na Mama yee Mama yee Mama kifi guda a cikin rafi Mama yee Mama yee Mama kaunar ki ta shiga ruhi na
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out