Lyrics

In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Dake naji na gamsu bazan yi bakar soyayya ba In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Da zuciya ta darsu da so ba'a ki a furta ba In dai zan iya numfashi bazan ki na bayyana kalma ba In naga abin haushi a zuci bazan mishi gurbi ba Inai miki rarrashi a rai banso kiji ciwo ba Mai kin ki gwada min shi bazan ki nayi mishi duka ba Burin ki gwada mini shi na dau hidima ban kosa ba In har mukayo sabo, baza naki damke amana ba In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Dake naji na gamsu bazan yi bakar soyayya ba Ruwa a cikin kurtu sanin yanayin shi wakilin shi A zuci akwai zance da sannu ka bini na furta shi Da kaji kalamai na ka yarda ka barni na furta shi Shi so fah muradi ne da rai ya aminta ya daura shi Bazan saki rashe ba na barka nawa kaina kyashi Sanar mini burin ka bazan ki na bika mu zauna ba In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Da zuciya ta darsu da so ba'a ki a furta ba Adon sama taurari awarwaro kyan shi a hannaye Fure da alamar su adon dawa kukan tsuntsaye A zuci akwai naso dake taba rai a shige maye Ki yarda ki lamunce ki sa na fahimta dani waye Kice mini kin karba mu shimfida son mu a kai waye Nayi miki madallah kiran ki bazan ki na amsa ba In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Dake naji na gamsu bazan yi bakar soyayya ba Rike ni muje taro yau na zama taka ka nuna ni Ka yarda kabar tsoro duk inda ka gamsu ka daura ni Kaine daya zabi na ganin ka yakan dada burge ni Zaman mu dakai tare na tabbata zai zama khairi ne Rikon jiya shine yau ina dada baka dalili ne Bazan kuma canza ba kace mini ban cika aiki ba In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Da zuciya ta darsu da so ba'a ki a furta ba Zan kyauta kalamai na da dada zan miki furtawa Na saki a dama na na lura dake ba kosawa Hakkin ki dare rana nayi alkawarin zan karewa Don ke kika min rana, a so har kin ka zamo tawa Sannan kika jajirce a bar mini ke ba canzawa Kiji ni ki lamunce ki yarda bazan miki koro ba In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Da zuciya ta darsu da so ba'a ki a furta ba In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Dake naji na gamsu bazan yi bakar soyayya ba In da so da akwai kauna ido bazai gaza kima ba Da zuciya ta darsu da so ba'a ki a furta ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out