Lyrics

Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa, hakane Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa Allahu ubangiji mai yanda yaso sarki daya (yan'uwa) Mai juyan lamura, mai dauke dare yayi safiya (yan'uwa) Shi yayi mini hikimar waka na biye ta gaba daya (yan'uwa) Toh yau na karkato fannin ilimi kuji gaskiya Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa Makaranta ginshiki na kira ta a waka yan'uwa (yan'uwa) Ilimi a ciki yake in muje zamu ga karuwa (yan'uwa) Komai ka gani a yau ilimi ne yayi masa garkuwa (yan'uwa) Ilimi saiti yake duk mai shi baya hayaniya, hakane Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa Sai kayo ilimi zaka san bautan Allah daya (yan'uwa) Tsarkin ka da alola daure leka islamiyya (yan'uwa) Sallah in zaka yo ilimi ne zai maka tsakiya (yan'uwa) Don sallar jahili matsala ce fal da hayaniya, a ciki Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa Ilimin boko shima a yau daya zam mana kariya (yan'uwa) In ka zauna babu shi wataran sai an maka dariya (yan'uwa) Ko aiki bai yo in ba ilimin boko daya (yan'uwa) Ni ina ta kulafuci jama ku mu tashi gaba daya, haka Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa Ni yau waka nake da babu sani da banyi ba (yan'uwa) An koyan fatiha, bismillah wacce nasa gaba (yan'uwa) Sannan ga A da B a fagen boko ba'a barni ba (yan'uwa) Naga ranar ilimi domin na tashi da tarbiyya, hakane Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa, hakane Makaranta ginshikin tsarin tafiya kan rayuwa Kuma neman ilimi tushen alkhairi yan'uwa, hakane
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out